Isa ga babban shafi
Venezuela

Venezuela: Kasashen yankin kudancin Amurka sun yi watsi da sabuwar Majalisa

Kasashen yankin kudancin Amurka da suka hada da Peru, Argentina, Brazil, Colombia da sauran kasashe 7 na yankin, sai kuma, Amurka, sun yi tur, tare da yin watsi da sabuwar majalisar dokokin kasar Venezuela da gwamnatin Nicolas Maduro ta kafa.

Wasu 'yan kasar Venezuela da ke cigaba da zanga zangar adawa da gwamnatin Maduro.
Wasu 'yan kasar Venezuela da ke cigaba da zanga zangar adawa da gwamnatin Maduro. Reuters
Talla

Sanarwar da shugabannin kasashen suka fitar, ta ce asu cigaba da daukar tsohuwar majalisar kasar ta Venezuela, da ‘yan adawa suka fi rinjaye, a matsayin halastacciya.

Matakin gamayyar kasashen ya zo ne, bayanda a jiya Juma’a, gwamnatin Maduro ta sanar da cewa sabuwar majalisar kasar zata fara aikin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

Shugaba Maduro ya zargi ‘yan dawar kasar da haddasa tashin hankalin da yayi sanadin rasa rayukan mutane 125.

Har yanzu dai al'ummar kasar suna cigaba da zanga-zangar neman Maduro ya sauka daga mukaminsa, yayinda jami’an tsaron kasar suke cigaba da arrangama da su.

A wani rahoto da ta wallafa majalisar dinkin duniya ta ce jami'an tsaron Venezuela suna yin amfani da karfi fiye da kima kan fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.