rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Italiya Eritrea Habasha Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Italiya: Jami'an tsaro sun kori bakin haure 800

media
Wasu daga cikin bakin haure 'yan Africa da jamia'n tsaron kasar Italiya suka kora daga wani sansanin wucin gadin da suke amfani da shi a birnin Rome. Ahram Online

Hukumar Kula da Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar damuwar ta kan yadda hukumomin birnin Rome suka kori wasu baki 800 ‘yan asalin kasashen Habasha da Eritrea, daga wani gini da suka samu a matsayin matsuguni na wucin gadi.


Hukumar tace 200 daga cikin wadanda aka kora da ginin akan titi suka kwana, a garin dake dauke da daruruwan bakin da basu da wurin zama.

Hukumar ta bukaci hukumomin birnin na Rome, da su taimaka wajen samawa bakin wurin zama.

Baki sama da 600,000 daga Afirka, Asiya da kuma Gabas ta Tsakiya suka ketara zuwa kasar Italiya daga shekarar 2014 domin neman mafaka.