Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya fara kamfen na manufofinsa a Turai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fara ziyara zuwa kasashen tsakiya da kudu masu gabashin Turai domin neman goyon bayansu ga wasu sabbin manufofinsa akan ci gaban tattalin arzikin Tarayyar Turai.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Reuters
Talla

Kasashen da shugaban zai ziyarta sun hada da Austria da Romania da Bulgaria.

Daga cikin bukatun Macron a ziyarar sun hada da sauya tsarin Tarayyar Turai da ke kamfanoni damar tura ma’aikata zuwa wasu mambobin kungiyar ba tare da biyan haraji ba.

Macron na son a takaita lokacin da ma’aikata daga mambobin Tarayyar Turai za su kwashe a wata kasa a nahiyar zuwa shekara daya.

Sannan daga cikin tsare tsaren akwai manufar yadda Tarayyar Turai za ta tantance kasashen da ya kamata su zuba jari a mambobinta Musamman yadda za su tunkari China ta yadda za a magance kwararar shigar da kayayyaki a nahiyar.

Mista Macron na son gwamnatocin Tarayyar Turai za su koma sayen kayayyakin da kamfanonin nahiyar ke samarwa ba tare da sun fita waje ba.

Ziyarar shugaban na zuwa a yayin da farin jininsa Faransa ya fara dushewa.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa kasha 37 kawai na Faransawa suka nuna jin dadin manufofin shugaban tun hawansa kan karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.