Isa ga babban shafi
Jamus

Kwararru a Jamus sun yi nasarar kwance bam din yakin duniya na 2

Gwanayen kwance bama bamai a kasar Jamus, sun yi nasarar kwance wani bam da Birtaniya da jefa a Frankfurt lokacin yakin duniya na biyu, wanda ba’a gano ba sai a makon da ya gabata.

Wani bam da bai fashe ba da aka gano a birnin Frankfurt ba Jamus, da aka jefa shi a lokacin yakin duniya na biyu.
Wani bam da bai fashe ba da aka gano a birnin Frankfurt ba Jamus, da aka jefa shi a lokacin yakin duniya na biyu. REUTERS/Ralph Orlowski
Talla

Kwance bam din ya tilasta kwashe mutane akalla 60,000 daga gidajen su, yayin da dubban masu aikin agaji suka bada gudummawa domin ganin jama’a basu fuskanci hadari ba.

Ana kyautata zaton cewa, jiragen yakin Birtaniya ne suka jefa bam din kirar HC 4000, yayin gwabza yaki da gwamnatin Nazi a lokacin yakin duniya na biyu, tsakanin shekarun 1939 zuwa 1945.

An gano bam din ne yayin aikin sabunta ginin wani sashin jami'ar da ke birnin na Frankfurt.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.