Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta soma amfani da jiragen yaki a Sahel

Faransa ta bayyana shirin amfani da jiragen sama masu sarrafa kansu domin kai hare-hare kan ‘yan ta’addan da ke barazana a Yankin Sahel.

Faransa za ta yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel da ya kunshi Nijar da Mali da Mouritania da Chadi
Faransa za ta yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel da ya kunshi Nijar da Mali da Mouritania da Chadi Reuters
Talla

Ministan tsaron kasar Florence Parley ta ce shugaba Emmanuel Macron ya mayar da yaki da ‘yan ta’adda a matsayin babbar manufarsa na kasashen waje kuma dalilin haka ya sa aka dauki matakin.

Yanzu haka Faransa na da irin wadannan jirage guda 5 a birnin Yammai da ke Jamhuriyar Nijar domin taimakawa sojojinta 4,000 d ake yaki da ta’addanci a Afirka.

Faransa ta ce jiragen yakin za su kasance babbar barazana ga ‘yan ta’adda.

Manyan kasashe kamar Amurka da Birtaniya da Isra’ila na da jiragen yaki a kasashe da ke fama da rikici kamar Syria da Yemen da Iraqi da Afghanistan da kuma Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.