Isa ga babban shafi
Turai

Kotun Turai ta yi watsi da bukatar Hungary da Slovakia kan 'yan gudun hijira

Babbar kotun Turai ta yi watsi da karar da Hungary da Slovakia suka shigar na kalubalantar tsarin karbar dubban 'yan gudun hijira da ke neman mafaka a kasashen na Turai. Hukumar Tarayyar Turai ta yaba da hukuncin Kotun, wanda yanzu ya tabbatar da tsarin raba 'yan gudun hijirar tskanin mambobin kungiyar.

'Yan gudun hijirar da galibinsu 'yan Afrika ne da 'yan gabas ta tsakiya da ke gujewa yaki a kasashensu na kwarara Nahiyar Turai ne ta Girka da Italiya.
'Yan gudun hijirar da galibinsu 'yan Afrika ne da 'yan gabas ta tsakiya da ke gujewa yaki a kasashensu na kwarara Nahiyar Turai ne ta Girka da Italiya. REUTERS
Talla

Duk da dai kotun ta yi watsi da koken na Hungary da Slovakia amma har yanzu kasashen biyu na ci gaba da adawa da matakin tilasta musu karbar 'yan gudun hijira, tun bayan amincewa da tsarin rarraba 'yan gudun hijira masu neman mafaka a yankunan Nahiyar ta Turai.

Har yanzu dai babu dan gudun hijira ko da mutum daya da kasar ta Hungary ta karba tun bayan kaddamar da shirin rarraba 'yan gudun hijirar  masu neman mafaka tsakanin kasashen.

Kasashen Turai dai sun amince da tsarin ne wanda ke da nufin rarraba 'yan gudun hijrar da ke kwararowa daga gabas ta tsakiya da Afrika sanadiyyar rikicin da ke faruwa a kasashensu, wadanda kuma ke kwarara nahiyar ta Girka da Italiya.

hukumar tarayyar Turai ta yi na'am a hukuncin kotun wanda ta ce ya zo dai dai da tsare-tsarenta don rage yawan 'yan gudun hijirar ta hanyar bai wa kowacce kasa na ta kason.

Sai dai kuma Hungary ta yi Ala wadai da hukuncin wanda ta bayyana a matsayin barazanar tsaro ga kasarta dama daukacin nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.