rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Birtaniya Ireland

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ireland za ta fuskanci kalubale a ficewar Birtaniya daga tarayyar Turai

media
Wakilin Tarayyar Turai Michael Barnier a tattaunawar ficewar Birtaniya REUTERS

Tawagar bangaren Tarayyar Turai da ke tattauna batun Ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai ta ce babban kalubalen da ke gabanta a yanzu shi ne makomar yankin Ireland. Jagoran tawagar Michel Barnier ya bayyana damuwa akan bukatar Birtaniya game da makomar arewacin Ireland da kuma iyakarta da jamhuriyar Ireland wacce mamba ce a Tarayyar Turai


Tawagar Turai kan tattauna ficewar Birtaniya sun wallafa manufarsu ne a yau kan makomar arewacin Ireland da kuma iyaka da Jamhuriyyar Ireland wacce mamba ce a Tarayyar Turai.

Michel Barnier ya ce ya shiryawa tattaunawar amma ya bayyana damuwa akan makomar iyakokin yankin Ireland.

A cikin sanarwar da wakilan na Turai suka wallafa sun ce hakkin Birtaniya ne ta warware matsalar kan iyakar yankin na Ireland.

Mista Bernier ya ce bukatar Birtaniya akan arewacin Ireland babbar damuwa ce.

Daga cikin bukatun, Birtaniya na son Tarayyar Turai ta dakatar amfani da dokokinta a yankin da tsarin kasuwanci na bai-daya wanda hakan zai nuna yankin ya fice daga cikin kungiyar.