rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Fursunoni Masu Hatsari Fiye Da 100 Sun Tsere Daga Birtania

media
Firaministan Birtaniya Theresa May rfi

Gwamnatin kasar Birtaniya ta ce fursunoni sama da 100 masu hatsarin gaske suka tsere daga gidan yari dake Tsubirin Virgin Islands yayin da mahaukaciyar ambaliyar ruwa da Iska ta ratsa yankunan Birtaniya


Karamin Ministan Waje  Alan Duncan ya shaidawa majalisar Britaniya cewa wannan tsubiri na Virgin Islands na cikin hatsari saboda tserewar wadannan fursunoni.

Ministan ya bayyana cewa an tura jami'an tsaro domin ganin an kama na kamawa da tabbatar da babu wani kazamin labari da ya auku.

A cewar Ministan,  Gwamnati ta yi kokari domin ganin mahaukaciyar ambaliyar ruwa da iska sun wuce kuma mutan 9 ne suka mutu bayan da ambaliyar ta wuce.