Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta rusa dokar bincike kan kisan kare dangin Rwanda

A Faransa, kotun fasalta kundin tsarin mulki ta rusa dokar da tsohon Shugaban kasar Francois Hollande ya dauka na bayar da dama tare da samu karin haske a takkardun bincike kan kisan kare dangin kasar Rwanda. Matakin da akasarin kungiyoyin kare hakkin bil adam suka yi tir da allah wa dai.

Masu fafutukar kare hakkin bil'adama dai na kallon sabon matakin kotun a matsayin wata manufa ta siyasa.
Masu fafutukar kare hakkin bil'adama dai na kallon sabon matakin kotun a matsayin wata manufa ta siyasa. Reuters
Talla

Kotun fasalta kudin tsarin mulkin Faransa a wani zaman ta na yau juma’a ta haramta dokar nan da ke kayyade tare da takaita bicinken takardu ko sheidu kisan kare dangin Rwanda daga tsoffin Shugabanin kasashe ko Firaministan dama wasu mukarraban Gwamnati.

Daukar wannan matakin dai ya biyo bayan hana wani malamin bincike Francois Graner damar samun karin haske tare da bicinke cikin wasu littatafai da ke karkashin fadar shugaban Faransa.

Tun a ranar 7 ga watan Afrilun shekarar 2015 ne fadar Shugaban kasar Faransa ta sanar da ba da damar samun cikkakun bayyanai daga cikin littatafan bincike dangane da kisan kare dangin Rwanda kama daga shekara ta 1990 zuwa 1995, dokar da ke zuwa daf da zagayowar shekaru 21 da aikata wannan kazamin aiki.

Matakin daga kotun fasalta kudin tsarin mulkin Faransa na yau na a matsayin kariya doka a cewar da dama daga cikin masu gwagwarmayar kare hakin bil adam, inda suka danganta hakan da cewa soke ko kuma haramata samun cikkakun bayanai a kan kasar ta Rwanda ya ta’alaka ne da siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.