Isa ga babban shafi
Faransa

Dan jarida Loup Bureau ya dawo Faransa

Yau lahadi ne dan jaridar nan bafaranshe mai suna Loup Bureau da ya share kusan kwanuki 50 a daure gidan maza a Turkiya ya samu komawa Faransa bayan da ya samu salama daga hukumomin Turkiya.

Dan jaridar Faransa  Loup Bureau yan lokuta bayan dawowar sa Faransa
Dan jaridar Faransa Loup Bureau yan lokuta bayan dawowar sa Faransa GEOFFROY VAN DER HASSELT / AFP
Talla

Ranar 26 ga wata yuli ne yan sandan Turkiya suka kama shi a kan iyakar kasar da Iraki ya na dauke da wasu hotuna dake nuna shi da mayakan kurdawa.

Turkiya na zargin wannan dan jarida da hada kai da kungiyoyin yan ta’ada,

Salamar dan jaridar na zuwa ne yan lokuta bayan ziyarar da Ministan harakokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya kai a Birnin Ankara tareda ganawa da hukumomin kasar ta Turkiya..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.