Mutane 5,000 ke mutuwa dalilin shakar gurbatacciyar Iska a Turai
Wani binciken masana yace akalla mutane 5,000 ke mutuwa a nahiyar turai kowacce shekara, sakamakon shakar iskar motocin dake amfani da gas ko man diesel suka gurbata.
Wallafawa ranar:
Binciken ya biyo bayan amincewar da kamfanin hada motocin Volkswagen yayi, cewar yana aikata almundahana wajen bayyana irin hayakin da motocinsa ke fitarwa a shekara ta 2015.
A watan Mayu na shekarar bana, wani binciken da aka wallafa a Mujallar Yanayi ya bayyana cewa mutane dubu 38,000 suka mutu sakamakon shakar irin wannan hayakin a fadin duniya a shekarar 2015.
Masu binciken daga kasashen Norway, Austria, Sweden da kuma Holland sun ce gurbacewar Muhalli na da nasaba da mutuwar kusan mutane 10,000 a Turai kowacce shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu