Isa ga babban shafi
Faransa

Zanga zangar adawa da sauyin dokar kwadago a Faransa

Masu adawa da sake fasallta dokokin aikin kwadago da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukata, a yau alhamis sun sake fantsama a kan titunan manyan biranen kasar, domin nuna adawa da matakin da gwamnatin ta dauka na son aiwatar da shirin.

Dandazon masu zanga zangar adawa da matakin gwamnatin shugaban Faransa Emmanuel Macron na sauye sauye a dokar kwadago ta kasar.
Dandazon masu zanga zangar adawa da matakin gwamnatin shugaban Faransa Emmanuel Macron na sauye sauye a dokar kwadago ta kasar. Reuters
Talla

Philippe Martinez, shine shugaban kungiyar kwadago ta CGT, da ta gudanar da zanga zanga a birnin paris, ya ce sun riga sun dauki niyar yin fito na fito da shirin yi wa dokokin aikin gyaran fuska.

Har ila yau Ma’aikatan da ke cike da fushi kan shirin sun gudanar da zanga zanga a wasu mayan birnanen kasar da suka hada da Marseille da ke kudu maso gabashin.

Kungiyar kwadago ta CGT, daya daga cikin manyan kungiyoyin da ke zanga zangar ce ta farko da ta gudanar da zanga zangar kara matsa kaimi ga gwamnati ana jajibirin gabatar da kudirin ga taron majalisar ministoci a gobe juma’a, da za ya tabbatar da aiki nan take da sabin dokokin kwadagon da aka samar.

A lokacin da yake tsokaci a tattaunawar da ya yi da tashar talabijin ta CNN a jiya laraba kan zanga zangar, matashin shugaban kasar na Fransa Emmanuel Macron ya bayyana yarda da demokradiya, sai dai a cewarsa demokradiya ba akan titi take ba, ya ce duk yana mutunta masu zanga zangar, to amma suma ya kamata su mutunta yancin faransawan da suka zabe shi ke da shi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.