rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus Angela Merkel Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Angela Merkel ta lashe zaben Jamus

media
waziriyar jamus Angela Merkel REUTERS/Fabrizio Bensch

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta lashe zaben da zai bata damar samun wa’adi na 4 bayan kammala shekaru 12 a karagar mulki.


Sakamakon farko na zaben da aka gabatar ya nuna cewar hadin guiwar Jam’iyyar ta na CDU/CSU sun samu kashi 33 na kuri’un da aka kada, yayin da Jam’iyar Social Democrat ta babban abokin adawar ta Martin Schulz ya zo na biyu da kashi 20-21.

Wani abin mamaki shine yadda Jam’iyyar dake yaki da addinin Islama ta AfD ta samu kashi 13 na kuri’un.