rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai ‘Yan gudun Hijira

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tarayyar Turai ta kaddamar da sabon shirin karbar 'yan ci rani

media
Karkashin sabon shirin Tarayyar Turai za ta gindaya karbar 'yan ci rani da 'yan gudun hijira kimanin dubu hamsin cikin shekara biyu. Reuters

Tarayyar Turai ta kaddamar da wani sabon shirin karbar baki ‘yan gudun hijira daga gabas tsakiya da kuma ‘yan ci ranin Afrika a wani mataki na haramta ratso tekun Bahrum mai hatsarin gaske inda kullum ake samun hasarar rayukan jama’a.


Shirin ya kunshi karbar ‘yan gudun hijira da ‘yan ci ranin Afrika nan da shekaru biyu a tsakanin mambobin Tarayyar Turai.

Babban jami’in kula da gudun hijira na Tarayyar Turai Dimitiris Abramopolous ya shaidawa taron manema labarai a Brussels cewa sun dauki matakin ne domin kawon karsshen hatsarin ratso tekun bahrum.

Hukumar Tarayyar Turai ta ce za ta bullo da tsarin karbar ‘yan ci ranin akalla dubu hamsim a shekaru biyu amma wadanda ke matukar bukatar taimakon kasashen duniya.

Akwai ‘yan gudun hijira dubu 23 da Tarayyar Turai ta karba da aka rarraba a sansanoni a mambobin kungiyar yawancinsu yan gudun hijirar rikicin Syria

Yanzu kuma Tarayyar Turai za ta mayar da hankali ga baki da ke kwarara daga Afrika yawanci daga Libya da Nijar da Masar da Chad da habasha da Sudan.