Majalisar Faransa na kada kuri'a kan yaki da ta'addanci
A wannan Talata ne Majalisar Dokokin Faransa za ta kada kuri’a dangane da sabuwar dokar yaki da ayyukan ta’addanci a kasar, lamarin da zai kawo karshen aiki da dokar ta baci da aka kafa tsawon shekaru biyu da suka gabata a kasar.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Emmanuel Macron ce ta gabatar da wannan sabon daftari a gaban Majalisar, lura da yadda wasu ke kallon dokar ta bacin da ake amfani da ita a tsawon shekaru biyu da cewa tana tauye hakkokin jama’ar kasar.
Christine Lazerges, shugabar hukummar kare hakkin bil’adama a kasar ta Faransa, ta ce aiki da dokar ta bacin ya kasance wata dama ta cin zarafi da kuma tauye wa jama’a hakkokinsu a tsawon wadannan shekaru biyu.
To sai dai ministan cikin gidan kasar Gerard Collomb, ya bayyana sabuwar dokar a matsayin wadda za ta taimaka wajen rage irin barazanar da kasar ke fuskanta daga ‘yan ta’adda da kuma masu tsatsaurar akida.
An dai fara amfani da dokar ta baci a kasar ne bayan harin da kai cikin watan nuwamba a birnin Paris inda aka samu asarar rayukan sama da mutane 130.
To sai dai kuma wasu na ganin cewa irin matakan da aka cusa a cikin sabuwar dokar wadda Majalisar Dokokin ke shirin tafka mahawara akai a wannan talata, matakai ne tsaurara da za su iya kawo cikas ga ‘yancin da jama’a suke da shi a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu