rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Jamus Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta goyi bayan hadakar Bankin PNB Paribas da Commerzbank na Jamus

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Reuters

Gwamnatin Faransa ta ce tana goyon bayan yunkurin da bankin PNB Paribas na neman hada guiwa da takwaransa na Commerzbank da ke kasar Jamus, a daidai lokacin da wasu bayanai ke cewa ita ma gwamnatin Jamus na goyon bayan wannan kusanci.


Kakakin gwmanatin na Faransa Christophe Castaner wanda ke zantawa da menama labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar ministocin kasar, ya ce siyasar da bankin na BNP Parisbas ke kan aiwatarwa don samar da kusanci da takwaransa na kasar Jamus Commmerzbank, abu ne da zai haifar da kyakkyawan sakamakon ga bankin.

Castaner, ya ce duk yake har yanzu bankunan biyu ba su cimma matsaya kan wannan batu ba, to amma tabbatuwarsa za ta kasance mai amfani ga bankin na BNP Paribas wanda gwamnatin Faransa ke da hannayen jari a cikinsa.

Makonni biyu da suka gabata, ministan kudin Jamus, ya bayyana cewa kasar na shirin sayar da kusan kashi 16 cikin dari na hannayen jarin da ta mallaka a bankin na Commerzbank.

A shekara ta 2009 ne gwamnatin Berlin ta karbi ragamar tafiyar da bankin domin kauce wa rugujewarsa sakamakon matsalar tattalin arziki da ta shafi yankin Turai da sauran sassan duniya.