Isa ga babban shafi
Spain

Yankin Catalonia na shirin sanar da ballewa daga Spain

Shugaban Yankin Catalonia da ke neamn ballewa daga kasar Spain Carles Puigdemont yace nan da karshen wannan mako Yankin zai bayyana ‘yancin cin gashin kai sakamakon zaben raba gardamar da mutanen yankin suka kada.

A ranar lahadi mutanen Catalonia suka kada kuri'ar ballewa daga Spain
A ranar lahadi mutanen Catalonia suka kada kuri'ar ballewa daga Spain REUTERS
Talla

Wannan matsayin na zuwa ne jim kadan bayan Sarki Felipe ya zargi shugabannin Catalonia da neman jefa kasar cikin rudani.

Gwamnatin Spain da babbar kotun kasar sun danganta zaben raba gardamar da aka gudanar a ranar Lahadi a matsayin haramtacce.

Amma shugabannin Catalonia sun ce sakamakon zaben ya nuna mutanen yankin sun amince a balle daga Spain.

Shugaban yankin a wata hira da kafar yada labaran Birtaniya ya ce nan da sa’o’I 48 za su sanar samun ‘yancin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.