rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Spain Catalonia Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta haramta zaman majalisar dokokin Catalonia

media
Taron masu zanga-zangar neman 'yancin yankin Catalonia REUTERS/Enrique Calvo

Kotu a Spain ta haramta wa Majalisar Dokokin Yankin Catalonia gudanar da wani zama a ranar litinin 9 ga wannan wata, wanda a lokacinsa ne ya kamata majalisar ta bayyana matsayinta dangane da sakamakon kuri’ar raba gardamar ballewar yankin.


Alkalan Kotun Tsarin Mulkin kasar ne suka amince da daukar wannan mataki da gagarumin rinjaye, bayan da jam’iyyar ‘yan gurguzu da ke mulkin kasar ta gabatar da bukatar hakan a gaban kotu.

A ranar litinin mai zuwa ne Majalisar Dokokin Yankin na Catalonia ta shirya gudanar da zama na musamman domin bayyana matsayinta dangane da sakamakon wannan zabe.

Matukar dai majalisar ta amince da sakamakon, wannan na nufin share fage ga gwamnatin yankin domin shelanta ‘yancin-kansa, matakin da kuma Spain ke cewa ya saba wa doka.