Isa ga babban shafi
spain

Al'ummar Catalonia na neman tattaunawar sulhu da gwamnati

Dubban al’ummar Spain ne yau Asabar suka gudanar da wata zanga-zanga a Madrid kan bukatar kawo karshen rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnatin kasar da yankin Catalonia, bayan bukatar yankin na ballewa daga kasar.A dai dai lokacin da yankin na Catalonia shi ma ke gudanar da makamanciyar zanga-zangar don neman tattaunawar sulhu da gwamnatin kasar bisa bukatar tabbatar da 'yancin yankin cikin lumana. 

A Talata mai zuwa ne al'ummar yankin na Catalonia ke sa ran shugaba Carles Puigdemont ya sanar da samuwar yancin yankin a matsayin kasa.
A Talata mai zuwa ne al'ummar yankin na Catalonia ke sa ran shugaba Carles Puigdemont ya sanar da samuwar yancin yankin a matsayin kasa. Reuters
Talla

Zanga-zangar wadda ta kunshi daruruwan masu fafutukar kare hakkin dan Adam da mata da kananan yara dauke da tutocin kasar sanye kuma da fararen kaya na bukatar ci gaba da kasancewar Spain a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Kawo yanzu dai ba a jiyo duriyar shugabannin yankin na Catalonia da suka sha alwashin samun ‘yancin yankin cikin kwanaki kalilan masu zuwa ba, inda kuma a bangare suma daruruwan al’ummar yankin na Catalonia ke gudanar da makamanciyar zanga-zangar a birnin Barcelona, kan bukatar tattaunawa da gwamnatin kasar dangane da batun ‘yancinsu.

Hakan dai na zuwa ne bayan sassan kasuwanci daban-daban na sanar da matakin dauke shalkwatarsu daga yankin na Catalonia zuwa wasu sassan kasar sakamakon rikicin siyasar da ya ke fuskanta.

A baya-bayan nan ne dai banki mafi girma a wato Caixa Bank ya sanar da janye harkokin gudanarwarsa daga yankin matukar ba a kawo karshen rikicin siyasar ba.

Talata mai zuwa ce ake sa ran shugaban yankin na Catalonia Carles Puigdemont zai sanar da samuwar yancin yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.