Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ba za ta amince da ‘yancin Catalonia ba

Faransa ta ce duniya ba za ta amince da kasar Catalonia ba idan har yankin ya tabbatar da ballewa daga Spain. Wannan na zuwa a yayin da shugabannin yankin ke fuskantar matsin lamba na su jingine kudirin sanar da cin gashin kai daga Spain a gobe Talata.

Catalonia na shirin ayyana cin gashin kai
Catalonia na shirin ayyana cin gashin kai REUTERS
Talla

Ministar kula da sha’anin Turai Natalie Loiseau ta fadi cewa idan har yankin Catalonia ya sanar da cin gashin kai to Faransa da Tarayar Turai ba za su goyi bayan matakin ba.

Ministar ta bukaci a sasanta rikicin na Catalonia ta hanyar tattaunawa.

A gobe Talata ake sa ran shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont zai ayyana tabbatar da samun ‘yancin Catalonia bayan kuri’ar raba gardama da mutanen yankin suka kada a ranar 1 ga watan Oktoba, zaben da gwamnatin Spain ta kira haramtacce.

Faransa ta yi gargadin cewa idan har Catalonia ya balle daga Spain, to yankin ba ya cikin Tarayyar Turai.

Yankin Catalonia dai na da matukar tasiri ga tattalin arzikin Spain, kuma yanzu rahotanni sun ce kamfanoni da dama sun fara ficewa saboda adawa da ballewar yankin daga Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.