Isa ga babban shafi
Spain

Catalonia ta jingine sanar da 'yancin kai

Shugaban Catalonia Carles Puigdemont ya bukaci tattaunawa da gwamnatin Madrid tare da jingine sanar da ‘yancin cin gashin kai daga Spain. Mista Puigdemont ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a zauran majalisar yankin.

Shugaban Yankin Catalonia Carles Puigdemont
Shugaban Yankin Catalonia Carles Puigdemont LLUIS GENE / AFP
Talla

Sanarwar Puigdemont cewa 'babu shaka sun cancanci ‘yanci kai amma zasu dakata domin bai wa Madrid daman tattaunawa' ta sanyaya gwiwar wadanda suka kasa kunne domin ji ko shugaban zai sanar da ballewar daga Spain duk da matsin lambar da suka fuskanta daga ciki da wajen kasar.

Carles Puigdemont ya bukaci tattaunawa da gwamnatin Madrid

Sai dai Kakakin gwamnatin Spain ya fitar da sanarwar da ke watsi da bukatar Puigdemont, wadda ke cewa dabara ce ta sanar da ‘yanci.

Shugabanni ‘yan siyasa kama daga Catalonia, Madrid da Turai sun nuna adawarsu da wannan yunkurin, da suke gani na iya jefa kasar cikin gagarumin tashin hankali irinsa mafi muni tun komawa salon mulkin demokuradiya a cikin shekarun 1970.

Suma Kasashen EU da suka zura ido kan neman ‘yancin Catalonia sun bayyana furgaban da barazanar da ballewar zata yi ga kungiyar da ke fama da batun ficewar Burtaniya daga cikinta.

Yanzu dai ana iya cewa ra’ayoyi ya sun ban-ban tsakanin masu tsokaci kan rikicin ballewar Catalonia wanda shine rabuwar kai irinsa na farko da Spain ta tsinci kanta a ciki tun samun ‘yanci.

Madrid dai ta sake jadada cewa babu wata tattaunawa da zatayi da Catalonia kan wannan bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.