Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

Macron ya bukaci Merkel da ta goyi bayan manufofinsa a EU

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bukaci takwararsa ta Jamus Angela Merkel da ta goyi bayan kokarinsa na ganin an aiwatar da sauye-sauye ga manufofin kungiyar Tarayyar Turai.

Angela Merkel ta Jamus tare da Emmanuel Macron na Faransa
Angela Merkel ta Jamus tare da Emmanuel Macron na Faransa JANEK SKARZYNSKI / AFP
Talla

Macron, wanda ke gabatar da jawabi a gaban daliban wata jami’a da ke birnin Frankfurt na kasar ta Jamus ya ce, yana fatan Merkel za ta goyi bayan manufofinsa na samar da sauyi musamman a bangaren tsaro da kimiya da makamashi da batun kwararar baki da kuma yaki da ayyukan ta’addanci a yankin.

Shugaban na Faransa ya ce, ba ta yadda za a samu nasarar aiwatar da irin wadannan sauye-sauye, sai idan kasashen yankin sun amince da tsarin kasafin kudi na bai-daya da zai yi la’akari da wadannan manufofi.

Manazarta na ganin cewa zai kasance abu mai wuya Emmanuel Macron ya yi nasarar samun goyon bayan Merkel dangane da batun samar da kasafin kudi na bai-daya, lura da cewa Jamus na nuna dari-dari sakamakon raunin sauran kasahen yankin na Turai a fagen tattalin arziki.

To sai dai Macron ya ce, ya kamata a cikin shekara daya mai zuwa kasashen na Turai su amince da shata manufa kafin lokacin gudanar da zaben ‘yan majalisar yankin wanda za a yi a shekara ta 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.