Manufofin Macron kan kwadago na samun goyon baya a Turai
Sabon shirin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatarwa kungiyar Tarayyar Turai na kaddamar da sauye sauye a harkokinta tsakanin kasashen kungiyar ya yi nasarar tsallake matakin farko, yayin da wasu ke ci gaba da sukar shirin.
Wallafawa ranar:
Tuni dai ministocin kwadagon kasashen kungiyar 28 su ka bayyana goyan bayansu ga shirin musamman kan batun da ya shafi ayyukan kwadago da kuma daukar ma’aikata.
Matukar dai shirin ya samu karbuwa tsakanin mambobin kungiyar zai bai wa kamfanoni damar tura ma’aikata wasu kasashe ba tare da biyan haraji ba, lamarin da wasu ke kallon a matsayin wata dama ta bai wa kamfanonin kofar da za su rika daukar ma’aikata daga Gabashin Turai a kudade kalilan.
A cewar ministan kwadagon Faransa, Muriel Penicaud amincewa shirin na Macron gagarumar nasara ce ga ilahirin Tarayyar Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu