Isa ga babban shafi
Cataloniya

Gwamnatin Madrid ta karbe jagorancin Cataloniya

Fira ministan kasar Spain Mariano Rajoy ya kira taron majalisar kasar na gaggawa jim kadan bayan da majalisar dokokin kasar ta amince ma gwamnati da ta karbe ragamar jagorancin yankin Cataloniya, inda majalisar yankin ta amince da kudurin ayyana ‘yancin kai.

Siyasar kasar Spain dangane da batun Cataloniya
Siyasar kasar Spain dangane da batun Cataloniya 路透社。
Talla

Mariano Rajoy ya ce ya dauki damarar dawo da doka a yankin na Catalonia.

Firaministan Spain na Magana ne jim kadan bayan kammala kada kuri’a a majalisar dokokin yankin.

Firaminista Rajoy, wanda ya bayar da wannan sanarwa a shafinsa na twitter, ya ce ya na kira ga dukkanin al’umma su kwantar da hankulansu, domin kuwa za a dawo da doka a yankin na Cataloniya.

Dubun-dubatan masu rajin ballewar yankin ne dai suka taru a kusa da majalisar dokokin Cataloniya suna murna tare da rera taken yankin, jim kadan bayan da majalisar ta zabi ficewa daga kasar ta Spain.

Magoya bayan ballewar yankin sun dangata zaman majalisar na yau da ba shida tasiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.