Isa ga babban shafi
Spain

Tsohon shugaban Catalonia ya bukaci hadin kan jam'iyyun adawa

Tsohon shugaban yankin Catalonia da gwamnatin Spain ta kora, ya bukaci jam’yyun da ke goyon bayan ballewa daga kasar da su hada kai domin tunkarar zaben watan Disamba, da gwamnatin ta Spain ta shirya gudanarwa.

Tsohon Shugaban yankin Catalonia da gwamnatin Spain ta kora, Carles Puigdemont, yayin gabatar da jawabi a birnin Brussels.
Tsohon Shugaban yankin Catalonia da gwamnatin Spain ta kora, Carles Puigdemont, yayin gabatar da jawabi a birnin Brussels. REUTERS/Yves Herman
Talla

A cewar Puigdemont, nasarar jam’iyyun ce kawai zata kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu da Spain kan fafutukar ballewa daga kasar.

A jiya Juma’a, wata kotun Spain da bai wa hukumomin tsaron kasar umarnin kamo mata tsohon shugaban na yankin Catalonia, wanda a yanzu ke kasar Belguim, saboda kin bayyana da yayi a gabanta don amsa wasu tambayoyi.

A baya dai jam’iyyun da ke neman ballewar catalonia daga Spain na da kujeru 72 daga cikin 135 na majalisar yankin, sai dai sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayi na baya-bayannan, ya nuna mai yiwuwa a zaben na watan decmber su samu koma baya na zuwa a matsayi na 4 ko 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.