Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar Faransa ta cire wa Le Pen rigar kariya

Majalisar dokokin Faransa ta cire wa shugabar jam’iyyar masu ra’ayin rikau a kasar Marine Le Pen, wanda hakan zai bai wa masu bincike damar sauraren ta dangane da wasu hotuna da ta wallafa na mutune uku da mayakan IS suka hallaka.

'Yar siyasar Faransa Marine Le Pen
'Yar siyasar Faransa Marine Le Pen REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Tun da jimawa ne bangaren shari’a a kasar ta Faransa ya bukaci Majalisar ta cire wa Marine Le Pen rigar kariyar, domin samun damar sauraren ta, biyo bayan wallafa wadannan hotuna da ta yi a shafinta na Twitter cikin watan disambar 2015.

A cikin wadannan hotuna, akwai wata gawa da mayakan kungiyar ta IS suka taka da motar yaki, yayin da a gefensa akwai gangar jikin wani mutum da aka fillewa kai sannan aka ajiye kan a gefe, yayin da a can kasa Le Pen ta rubuta cewa ‘’wannan ita ce kungiyar Daesh’’.

Kafin nan shugabar jam’iyyar ta masu zazzafan ra’ayi a siyasar Faransa, ta janye hoton James Foley Ba’amurke wanda kungiyar ta fillewa kai.

A martanin da ta fitar bayan da Majalisar kasar ta sanar da cire ma ta rigar kariyar, Marine Le Pen ta bayyana matakin a matsayin siyasa da nufin zubar da mutucinta.

Le Pen ta ce cire ma ta rigar kariya na nufin cewa wadanda suka je Syria domin yin jihadi sannan suka dawo kasar sun fi ta mutunci a wajen ‘yan majalisar da suka dauki wannan mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.