Isa ga babban shafi
Faransa

Kyautatawa marasa galihu zai magance tsattsauran ra'ayi - Macron

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana wasu tsare tsaren da gwamnatinsa ta shirya da yake fatan za su kawar da talauci da kuma rungumar tsattsauran ra’ayin addini a yankunan marasa galihu da ke sassan kasar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin da yake jawabi a garin Tourcoing, da ke arewacin kasar ranar Talata, 14 ga Nuwamba, 2017.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin da yake jawabi a garin Tourcoing, da ke arewacin kasar ranar Talata, 14 ga Nuwamba, 2017. AFP/Julia Pavesi/Jerome Rivet/Katy Lee
Talla

Shugaban ya bayyana haka ne a garin Tourcoing, da ke bakin iyakar kasar da Belgium, yayinda ya ziyarci yankin, don musanta zargin da ‘yan adawa ke yi na cewa ba ya kula da masu karamin karfi.

Tsare-tsaren da shugaba Macron ke son aiwatarwa sun hada da samar da ingantaccen tsaro, bayar da tallafi na musamman ga mata masu yara, da kuma karfafa wa kamfanoni gwiwa domin su rika daukar ma’aikata daga yankunan marasa galihu.

Shugaban kasar ya ce yana son kawo sauyi nan da karshen wa’adin mulkinsa, inda ya nuna damuwarsa kan yadda yankunan marasa galihun suka yi kaurin suna wurin ayyukan assha.

Macron ya yi zargin cewa gazawar gwamnati na daga cikin dalilan da suka haifar da masu tsattsauran ra’ayi a yankunan ‘yan gudun hijira da suka shigo kasar, wanda hakan ya sanya matasa suke shiga kungiyoyin jihadi a kasashen Syria da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.