Ana dakon isar Hariri a Faransa ranar asabar
A ranar asabar ta wannan mako ake dakon isar Sa’ad Hariri, wanda ya yi ikirarin yin murabus daga mukaminsa na Firaministan Libanan zai isa birnin Paris na Faransa, a wani mataki na shirya tattaunawa domin warware rikicin siyasar kasar.
Wallafawa ranar:
A ranar alhmis ne ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya gana da firaministan na Libanan a birnin Riyad na Saudiyya kasar da daga can ne ya sanar da yin marabus.
A birnin Paris kuwa za a gana tsakanin Hariri da Emmanuel Macron a fadar Elysees, yayin da shugaban kasar ta Libanan Michel Aoun ke cewa ya zama wajibi firaministan ya dawo gida domin warware sabanin ko kuma yin marabus a gida amma ba daga waje ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu