Isa ga babban shafi
Jamus

Jam'iyyar SPD zata tattauna da Angela Merkel kan kawance

Niels Annen, wani jigo a babbar jam’iyyar adawa ta SPD ta Jamus, ya ce mai yiwuwa, jam’iyyar ta amince da sabunta kawancen kafa gwamnati ta shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel, idan suka gamsu da tayin da zata gabatar musu.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel yayin da ta halarci taro tattaunawa tsakanin jam'iyyarta ta CDU da ta ke jagoranta da kuma jam'iyyar CSU a Bundestag da ke birnin Berlin. 20 ga Nuwamba, 20, 2017.
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel yayin da ta halarci taro tattaunawa tsakanin jam'iyyarta ta CDU da ta ke jagoranta da kuma jam'iyyar CSU a Bundestag da ke birnin Berlin. 20 ga Nuwamba, 20, 2017. © REUTERS/Axel Schmidt
Talla

A ranar Juma’a shugaban jam’iyyar adawar ta SPD Martin Schulz ya amince ya tattauna da Merkel bisa kokarinta na ganin jam’iyyar ta sabunta kawancen da suka kulla na kafa gwamnati tun daga shekarar 2013.

Sai dai Schulz ya ‘ya’yan jam’iyyar ne zasu yanke hukuncin karshe kan yiwuwar sabunta kawancen.

A makon da ya gabata kokarin Angela Merkel na kafa sabuwar gwamatin hadin-kai, ya gaza bayan rushewar tattaunawarta ta jam’iyyar FDP lamarin da ke neman tursasawa kasar sake gudanar da sabon zaben.

Rikicin siyasar da Jamus ke neman fadawa zai hana gwamnatin Merkel daukar matakai ko umarni a cikin gida dama nahiyar turai baki daya, har sai an sake wani sabon zabe.

Merkel, wadda tsarinta na karbar bakin haure ya gamu da rabuwar kawuna, dole yasa ta ke neman kawance da wasu jam’iyyun adawa, la’akari da cewa bata samu rinjaye a zaben kasar da ya gabata ba.

Sai dai bayan shafe sama da wata guda tana fadi tashin ganin ta cimma yarjejeniyar, jam’iyyar FDP ta janye daga tattaunawar a makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.