Isa ga babban shafi
Spain

Puigdemont ya nemi 'yan Catalonia su jajirce kan 'yancin yankin

Tubabben shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont ya kaddamar da wani gangamin Kamfe a yau Asabar inda ya bukaci al’ummar yankin su san wanda za su zama don tabbatuwar batun ‘yancinsu.

Yayin gangamin na yau da Puigdemont ya gudanar a Brussels ya nemi al'ummar Catalonia su zabi wanda zai dora kan fafutukar nemarwa yankin 'yancin zama kasa mai cin gashin kanta.
Yayin gangamin na yau da Puigdemont ya gudanar a Brussels ya nemi al'ummar Catalonia su zabi wanda zai dora kan fafutukar nemarwa yankin 'yancin zama kasa mai cin gashin kanta. Reuters
Talla

A jawaban da Puigdemont ya gabatar yayin gangamin daya gudana a Belgium, ya ce lokaci yayi da ‘yan Catalonia za su kara nuna jajircewarsu kan bukatar da su ke da ita na zamowar yankin kasa mai cin gashin kan ta.

Ya ce tirjiyar da al’ummar suka nuna a baya ya fito da zahirin karfin da su ke da shin a zamowa kasa mai cin gashin kan ta, yana mai cewa kuma hakan zai tabbata ranar 21 ga watan Disamba mai zuwa.

Puigdemont wanda ke gudun hijira a Belgium tun bayan kwace kwarya-kwaryan ikon da Spain ta yiwa yankin na Catalonia a ranar 27 ga watan Oktoba, yanzu haka Spain na zarginsa da cin amanar kasa, amfani da kudade a wurin da basu dace ba, baya ga amfani da kujerarsa wajen tunzura al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.