rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Birtaniya da EU sun yi baran-baran a ganawarsu

media
Firaministar Birtaniya Theresa May da shugaban Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker REUTERS/Yves Herman

Tarayyar Turai da Birtaniya sun gaza cimma yarjejeniya a tattaunawar da suka yi jiya Litinin a birnin Brussels, to sai dai bangarorin biyu na da kyakkyawan fatan warware sabanin da ke tsakaninsu kafin karshen wannan mako.


Abubuwa uku ne suka hana cimma yarjejeniyar, da suka hada da yadda alaka za ta kasance tsakanin Turai da yankin Ireland, biyan basusukan da ke wuyan Birtaniya da kuma makomar ‘yan asalin Turai da ke zaune a Birtaniya.

Ganawar na zuwa ne bayan kungiyar Tarayyar Turai ta bai wa Birtaniya wa’adin gaggauta gabatar da gamsassun sharuddan ficewa daga nahiyar.

A bara ne dai Birtaniya ta kada kuri’ar ficewa daga Turai kuma ana saran kammala ficewarta a cikin watan Maris na shekarar 2019, sai dai har yanzu bangarorin biyu ba su kai ga cimma matsaya ba.