rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Vladimir Putin

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Putin zai sake takara a Rasha

media
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin REUTERS/Sergei Karpukhin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewar zai tsaya takarar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa wanda zai bashi damar samun Karin shekaru 6 a karagar mulki.


Shugaba Putin ya sanar da haka ne lokacin da ya kai ziyara wani kamfanin man kasar, inda ya ce zai gabatar da kan sa a matsayin dan takarar zaben da za’ayi a watan Maris na shekara ta 2018.

Idan ya samu nasara, Putin zai ci gaba da mulki zuwa shekara ta 2024.

Shugaba Putin ya hau karagar mulki a shekarar 1999 inda ya jagoranci Rasha zuwa shekara ta 2008 da ya mikawa Dmitry Medvedev, ya kuma zama Firaminista.

A shekarar 2012 Putin ya sake dawowa shugaban Rasha inda ya taimakawa kasar bunkasa tattalin arzikin ta duk da takunkumin da kasashen Turai suka kakaba mata.