Isa ga babban shafi
Faransa

Ana tuhumar tsohon shugaban Lafarge da ayyukan ta’addanci

An fara tuhumar tsohon Shugaban kamfanin siminti na Lafarge mallakin kasar Faransa Bruno Lafont da manyan ma’aikatanshi biyu kan zargin taimakawa ayyukan ta’addancin ta boyayyiyar hanya a Syria.

The logo of the French concrete maker Lafarge is seen on a plant in Paris, France, on May 22, 2017.
The logo of the French concrete maker Lafarge is seen on a plant in Paris, France, on May 22, 2017. Reuters/Gonzalo Fuentes
Talla

Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa baya ga Lapont akwai kuma wasu manyan jami’an kamfanin na Lafarge biyu da suka hadar da tsohon babban manajan da ke kula da ma’aikata Eric Olsen da kuma da kuma tsohon manajan Darakta Christian Herrault .

Yanzu haka dai ana zargin tsoffin shugabannin da biyan wasu makudan kudade ga kungiyar IS dama sauran kungiyoyin ta’addanci ta yadda reshen kamfanin da ke Jalabiya a Syria zai ci gaba da gudanar da ayyukansa duk da yakin da kasar ke fama da shi.

Lafont dai ya jagoranci kamfanin na Lafarge daga shekarar 2006 zuwa 2015 , lokacin da kamfanin ya hade da wani kamfanin kasar Sweden Holcim mai sarrafa kayan gine-gine inda ya sauya suna zuwa LafargeHolcim har zuwa watan Afrilun shekara ta 2017.

Binciken da hukumomi suka tsananta yanzu haka shi ne gano ko Lafont na da masaniya kan biliyoyin dalolin da kamfanin ke bai wa kungiyoyin ta’addanci na duniya.

Ko a makonni biyu da suka gabata an tuhumi wasu manyan tsoffin jami’an kamfanin 3 da ke Jalabiya da makamancin wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.