Faransa ta kwashi rukunin farko na ‘yan ci-rani daga Afirka
Kasar Faransa ta karbi rukunin farko na bakin da ke neman rayuwa mai inganci da ta dauko daga Afirka, bayan an tan-tance su daga cibiyoyin da ta kafa a nahiyar.
Wallafawa ranar:
Shirin da za ‘a dau tsawon shekaru ana gudanarwa na daga cikin sabon tsarin da kasar Faransa ta soma na karba bakin da suka cancanci shiga kasarta, domin rage mace-macen baki a tekun Baharum.
Wani dan kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da ke cikin baki 19 da kasar ta karba, Djamal tare da matar sa da kuma yaran sa guda 4 sun sauka a tashar jiragen Charles de Gaulle bayan sun kwashe shekaru 4 a sansanin ‘yan gudun hijira.
Zalika akwai wasu 'yan kasar Sudan da suka samu mafaka a Chadi sakamakon rikicin Yankin Darfur da suma suka samu mafaka yanzu haka a Faransa.
Shirin zai bai wa baki dubu 3 ‘yan Afirka daman shiga kasar kafin shekara ta 2019, da kuma rage alkalluman mutane da ke sa rayuwarsu cikin hatsari don shiga turai ta Teku.
Duban Baki suka rasa rayukansu a kokarin tsallake tekun Baharum tun tsanartar rikicin kwararan Bakin-Haure zuwa Turai a 2015, kamar yadda kungiyar ‘yan gudun hijira ta duniya ta tabbatar.
Sai dai Sabon shirin na Faransa zai kore Bakin da basu da cancantar samun mafaka a kasar, batun da ke fuskantar suka musamman daga kungiyoyin agaji da ke bai wa Bakin matsugunai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu