Isa ga babban shafi
Faransa

Macron yana fuskantar sabon kalubale kan rashin aikin yi a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gamu da mummunar suka kan sabon shirin da yake son aiwatarwa, wanda ake ganin zai hana marasa ayyukan yi damar karbar tallafin da suke samu kowanne wata.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. ludovic MARIN / AFP
Talla

Jaridar Canard Enchaine, ta ruwaito wata wasika da shugaban ya rubuta wadda zata tilastawa marasa ayyukan yi bayani kan kokarin da suke na neman aiki a kowanne wata kafin basu tallafi.

Faransawa na kallon matakin a matsayin wani yunkuri na dakile taimakon da ake yi wa marasa aikin yi a kasar.

Tun bayan zaben Emmanuel Macron a matsayin shugaban kasa, matsalar rashin aikin yi a Faransa ta karu da akalla sama da kashi 9.6 fiye da yadda abin yake kasashen Birtaniya da Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.