Faransa ta amince da tsananta bincike a iyakoki
Majalisar ƙoli a Faransa ta bayyana amincewarta da matakan tsananta bicinke a kan iyakokin yankin Turai, abinda ke ci gaba da janyo fushi daga ƙungiyoyin da ke kare hakkin baƙin haure.
Wallafawa ranar:
Majlisar ta ce ta dauki wannan mataki ne a wani yunƙuri na yaƙi da ta’adanci a yankin Turai, ta kuma buƙaci gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da dokar.
Ta kuma nuna buƙatar ganin jami’an tsaro sun mayar da hankali wajen tattance duk masu yunƙurin shiga nahiyar ta Turai.
Ƙungiyoyin da ke kare haƙƙokin yan cin-rani ne suka shigar da koke a majalisar ƙolin ƙasar, kan cewa gwamnati na amfani da ƙarfi fiye da ƙima zuwa a kan masu tafiya ci-rani, inda ta buƙaci gwamnati ta soke matakin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu