Isa ga babban shafi

Guguwar Eleanor ta yi kisa a Kasashen Faransa da Spain

Guguguwa mai karfin gaske dauke da ruwan sama na ci gaba da sauka a wasu kasashe da ke yankin yammacin Turai, inda ta yi kisa a Faransa da Spain tare da haifar da tsaiko ga harkokin yau da kullum, musamman a garuruwan da ke gabar teku.

Guguwar Eleanor na barnar a kasashen Turai
Guguwar Eleanor na barnar a kasashen Turai FRANCOIS LO PRESTI / AFP
Talla

Guguwar da aka yi wa Sunan ‘Eleanor’ mai gudun sama da kilomita 160 a kowacce sa’a daya, ta haddasa tsaiko ga jama’a a kasashen Birtaniya da Switzeland da Jamus da Belgium da kuma Hollande tare da raunata mutum 26.

Guguwar ta kuma haddasa tashin gobarar daji a Corsica daya daga cikin manyan yankunan da ke karkashin kasar Faransa. A halin yanzu an tura jirage masu saukar ungulu da jami’an kashe gobara masu yawan gaske domin shawo kan wutar dajin.

Guguwar Eleanor ita ce irinta ta hudu cikin sanyin hunturu da ta afkawa sassan nahiyar turai tun daga watan Disamban shekarar da ta gabata.

Sama da gidaje 29,000 ne a Faransa har yanzu basu da wutar lantarki sakamakon Eleanor da ta jikkata sama da ‘yan kasar 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.