rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya yi watsi da sabon littafin da ke sukar gwamnatinsa

media
Shugaban Amurka Donald Trump a lokacin da yake magana da na hannun damansa Steve Bannon, wanda a yanzu suka raba gari, yayin bikin rantsar da shi a watan Janairu, 2017. REUTERS/Carlos Barria

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da littafin da ke kunshe da bayanan batanci game da yakin neman zabensa da kuma gwamnatinsa, in da ya ce, littafin na cike da kare-rayi.


Ana saran fitar da littafin mai suna “Fire and Fury: inside the Trump White House” a ranar Juma’a, wanda Michael Wolf ya rubuta, duk da cewa gwamnatin Trump ta yi kokarin dakile fitar da littafin.

Lauyan shugaban Amuka ne ya jagoranci yunkurin hana kaddamar da wannan littafi wanda marubucin ya tattaro kalaman wani tsohon na hannun daman Trump Steve Bannon, da ke nuna Shugaba Trump bai dace da shugabancin kasar ba.

Littafin ya ruwaito Bannon yana zargin babban dan Donald Trump, Trump Junior, da yin mu’amulla da wani Lauyan Russia, zalika ‘yar shugaban kasar Ivanka tamkar kurma take a cewar Bannon.

Bayanai na cewa shugaba Donald Trump ya harzuka matuka da yadda tsohon na hannun daman nasa ya kwance masa zani a kasuwa, duk da cewa alakarsu tana da karfi sosai, hakan yasa Trump yin barazanar shigar da kara don neman hakkinsa a kotu.

Tun kafin su kaiga haka shugaba Trump ya bayyana Steve Bannon da cewa tababbe ne, wanda bai san abinda ya ke ba.

A watan Augusta ne dai Steve Bannon ya rabu da fadar gwamnatin Amurkan, bayan da aka yi masa korar kare.