Faransa ta yi bikin tunawa da harin da ya girgiza ta
Mujahidai guda biyu ƴan asalin ƙasar Faransa, masu biyayya ga ƙungiyar al-Qaeda ne suka kai harin a shekara ta 2015, inda suka kashe ma’aikata 11 domin nuna fushinsu game da irin ba’ar da mujallar Charlie Hebdo ke yi ga batutuwa na musulunci da kuma annabi Muhammad.
Wallafawa ranar:
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ajiye furanni a gaban tsohon ofishin kamfanin mujallar, a wani biki na tunawa da shekaru 3 bayan kai harin wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka
Harin wanda aka kai wa mujallar shi ne ya zamo kamar ɗan-ba na jerin hare-haren ta'addanci da aka kai wa ƙasar ta Faransa, waɗanda suka haifar da asarar ɗaruruwan rayuka.
Bikin wanda ya gudana a ranar Lahadi ya samu halarcin ma’aikatan mujallar ta Charlie Hebdo da jami’an gwamnati da kuma magajin garin birnin Paris Anne Hidalgo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu