Isa ga babban shafi
Turai

Turai za ta dauki matakin bai-ɗaya kan baƙin-haure

Shugabannin ƙasashe 7 na kudancin nahiyar Turai sun sha alwashin magance matsalar kwararowar baƙin-haure daga ƙasashen da yaki ya ɗaiɗaita da kuma ƙasashe marasa ƙarfi.

Bakin-haure masu son tsallakawa zuwa kasashen Turai.
Bakin-haure masu son tsallakawa zuwa kasashen Turai. REUTERS/Hani Amara
Talla

Kasashen sun ɗauki wannan alƙawari ne a ranar Laraba, bayan wani taro da suka gudanar a birnin Roma, inda suka tattauna matsaloli da dama da ke addabar yankin nasu.

Firaministan Italiya Paolo Gentiloni, wanda ƙasarsa ke cikin waɗanda suka fi fama da matsalar ta kwararowar baƙi, ya tabbatar da cewa an samu ci gaba game da rage kwararowar baƙin na haure da kuma safarar mutane, sai dai ya buƙaci tarayyar Turai ta yunƙura wajen ganin an inganta tsarin.

Shugabannin ƙasashen da suka haɗu a birnin na Roma domin tattauna wannan al’amari sun haɗa da na Cyprus, da Faransa, da Girka, da Italiya, da Malta, da Portugal, da kuma Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.