rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Birtaniya Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Faransa ba za ta amince a kafa sansanin bakin haure ba"

media
Shugaban Faranse Emmanuel Macron a yayin ziyararsa a yankin Calais Reuters

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, gwamnatinsa ba za ta amince da sake kafa wani sansanin bakin haure ba makamancin na dajin Calais a yankin arewacin kasar.


Macron ya bayyana haka ne a yayin gabatar da jawabi a ziyarar da ya kai yankin a dai dai lokacin da gwamnatinsa ke matsin lamba kan Birtaniya don ganin ta kara kaimi wajen bada gudun mawar daukan dawainiyar bakin hauren da ke kokarin shiga Birtaniya ta barauniyar hanya.

A cewar Macron, sun yi duk abin da ya kamata don hana bakin tsallakawa Birtaniya ba bisa ka’ida ba, kuma ya ce, ba za a yi amfani da dajin Calais ba a matsayin hanyar shiga Birtaniya ta bayan fage.

Tsohuwar gwamnatin Francois Hollande ce ta rusa sansanin na Calais mai cike da kazanta wanda ya kasance matsuguni ga bakin haure dubu 10

Sai dai har yanzu akwai tsirarun mutane da ke fakewa a sansanin da nufin samun sararin tsallakawa zuwa Birtaniya.