rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Italiya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 3 sun mutu a haɗarin jirgin kasa

media
Jami'an kamfanin safarar jiragen kasa na Italiya ba su yi karin haske kan hadarin ba. Courtesy of Felix Rios /via REUTERS

Aƙalla mutane 3 ne aka ruwaito sun mutu a kusa da Milan na ƙasar Italiya sanadiyyar haɗarin jirgin ƙasa da ya faru a safiyar Alhamis.


Kamfanin safarar jiragen ƙasa na Italiya ya bayar da sanarwar cewa jirgin ya goce daga kan layinsa ne a wani wuri da ke da nisan kilomita 40 daga birnin na Milan.

Masu ayyukan bayar da ceto sun ce mutane 10 sun samu munanan raunuka yayin da wasu da dama suka samu ƙanana raunuka.

Hotunan bidiyo sun nuna yan kwana-kwana na kokarin zaro waɗanda suka maƙale cikin taragan jirgin.