An haramtawa ‘yan majalisun sanya kayan da suke nuna alamar addini
Majalisar dokokin Faransa ta haramtawa ‘yan majalisun kasar sanya kayan da suke nuna alamar addini, a karkashin wani sabon tsarin ko dokar fayyace irin kayan da zasu rika shiga zauren majalisar da su.
Wallafawa ranar:
Tuni dai matakin ya fara fuskantar suka daga bangarori daban daban a Faransa.
Kakakin Majalisar ta Faransa Francois de Rugy, ya kare matakin da cewa, bai take hakkin kowa ba, wani bangare ne daga cikin dokar da aka kafa ta shekarar 2004, da ta haramtawa Malaman makarantun kasar da dalibai sanya dukkanin wata alama ta nuna addini.
Yanzu haka dai wasu ‘yan siyasar kasar na goyon bayan matakin na majalisar Faransa da kuma neman a fadada shi zuwa jami’o’i da wuraren aiki, wasu na kallon matakin ta fuskar cewa wani yunkuri ne kawai na fadada dakile ‘yancin addini.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu