Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya gargaɗi duniya kan yarjeniyoyin kasuwanci na 'danniya'

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da aiwatar da ƙa’idojinta na kasuwanci domin dawo da martabar harkar saye da sayarwa.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump a wurin taron tattalin arziki na duniya a Davos.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump a wurin taron tattalin arziki na duniya a Davos. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Trump wanda shi ne shugaban Amurka na farko da ya gabatar da jawabi a taron tattalin arziƙin duniya cikin shekaru 18 ya ce amma ƙofofin Amurka a bude suke ga ƴan-kasuwa.

Ya kuma ce ƙasarsa ba za ta amince da abinda ya kira 'makafin' yarjeniyoyin kasuwanci ba.

A wani jawabi da ya gabatar gab da rufe taron wanda aka yi a birnin Davos, shugaban na Amurka ya ce zai ci gaba da yaɗa aƙidarsa ta fifita Amurka a kan kowace ƙasa kamar yadda yake tsammanin dukkanin shugabanni za su fifita nasu ƙasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.