rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Spain Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Spain ta dakatar da shirin rantsar da Puidgemont

media
Tsohon shugaban yankin Catalonia Carles Puidgemont. REUTERS/Yves Herman

Kotun kundin tsarin mulki a Spain ta ce tsohon jagoran yankin Catalonia mai ƙoƙarin sake komawa kan muƙamin nasa zai iya samun hakan ne kawai idan ya je majalisa da kansa tare da samun izinin kotu.


Yanzu haka dai mutumin, Carles Puidgemont na gudun hijira ne a Belgium bayan da hukumomin Spain ke neman sa ruwa a jallo bisa zargin jagorantar yi wa gwamnati tawaye.

Sai dai ana sa ran majalisar yankin za ta kaɗa ƙuri’ar amincewa da shi a matsayin ɗan takaran shugaban yankin.

Wannan mataki na kotu dai babban koma baya ne ga masu rajin tabbatar da yancin yankin waɗanda ke ƙoƙrain ganin Puidgemont ya koma kan muƙamin.