rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Vladimir Putin Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan sandan Rasha sun kame jagoran 'yan adawa

media
Wasu magoya bayan jagoran 'yan adawar kasar Rasha Alexie Navalny, yayin da suka fito zanga-zangar da ya kira. Vladimir Bondarev/RFI

'Yan sandan Rasha sun kame jagoran ‘yan adawar kasar Alexie Navalny, jim kadan bayan da ya isa wurin da dubban magoya bayansa suka taro don soma zanga-zangar adawa da gwamnati.


A farkon watan da muke ciki, Navalny, wanda kotu ta haramta mishi tsayawa takarar shugabancin kasar, ya bukaci magoya bayansa da su yi fitar dango a wannan Lahadi, domin zanga-zangar rashin yarda da zaben shugaban kasar da zai gudana a ranar 18 ga watan Maris, wanda ya ce shugaban Rasha Vladmir Putin zai tafka magudi.

‘Yan adawa sun shirya gudanar da zanga-zanga a biranen Rasha akalla dari domin amsa kiran jagoran nasu.

Kafin kame Navalny, sai da ‘yan sandan kasar suka kai samame zuwa wasu ofisoshinsa, kuma zuwa yanzu ana tsare da akalla magoya bayansa 27.