rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nahiyar Turai za ta fuskanci ambaliyar ruwa

media
Kogin Seine a Paris na kasar Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes

Masu binciken yanayi sun yi gargadi samun mummunar ambaliyar ruwa a yankunan Turai saboda matsalolin dumamar yanayi, batun da ke zuwa kwanuki kadan da fuskantar ambaliya da kogin Seine na Paris ya haifar.


Ambaliyar ruwan da akayi hasashen kogunan Turai zasu haifar zai haifar da asara da dama, sama da wanda aka fuskanta a shekarar da ta gabata, sakamakon matsalolin dumamar yanayi da ke ci gaba da barazanar ga muhalli.

Hasashen da masana suka wallafa a wata mujalar yanayi na cewa, asaran da za a tafka na iya kai wa dala biliyan 19.

Rahotan ya ce alkaluman mutane da ambaliyar za ta shafa zai karu da kashi 86 cikin 100 wadda aka kiyasta a kan mutane dubu 650 a shekara.

Matsalar ambaliyar ruwa ta kasance daya daga cikin iftila’i da ke haddasa asara a Turai.

Wannan na daga cikin dalilan da ya sanya yarjejeniyar Paris na shekara ta 2015 cim-ma yarjejeniyoyin da ke ci gaba da kasancewa barazanar da haifar da dumamar yanayi.