Isa ga babban shafi
Brexit

May za ta gabatarwa Majalissa kundin yarjejeniyar Brexit

Friministan Burtaniya Theresa May ta ce za ta gabatarwa majalisar dokokin kasar kundin tsare-tsaren ficewar kasar daga Turai a hukumance kafin ta bukaci amincewarsu, tare da watsi da rahotannin da ke cewar tattalin arzikin kasar zai fuskanci tabarbarewa karkashin yarjejeniyoyin rabuwar da EU.

Firaministan Burtaniya Theresa May
Firaministan Burtaniya Theresa May REUTERS/Toby Melville
Talla

Kalaman Theresea May na zuwa ne bayan Jaridar Buzzfeed ta rawaito cewar tattalin arzikin Burtaniya zai fuskanci tabarbarewa ko da ta bar EU da yarjejeniyar kasuwanci, ko tsarin cinikin bai-daya a wani nazari da ta yi kan gwamnatin Burtaniya.

Sai dai Friministan da ke watsi da rahotan, ta ce nazarin da jaridar ta yi, fasara ce mara tushe. May ta ce sai ‘yan majalisun dokokin kasar sun yi nazari kan yarjejeniyar da kasar ta cim-ma da EU kafin su shiga kada kuri’ar nuna amincewarsu ko watsi da batutuwan yarjejeniyar ta kunsa.

May da ke jawabi a gaban manema labarai a ziyarar kasuwancin da ta kai China ta ce idan lokaci ya yi, majalisar dokokin kasar zata gabatar da nata tsarin wanda a kan haka ne za a yanke hukuncin karshe.

Kuri’ar da ‘yan Majalissun kasar za su kada shi ne zai tabbatar da matsayin ficewar kasar da ga EU. Ko da dai har yanzu ba a tsayar da ranar ba, amma ana saran a gudanar da shi bayan cim-ma yarjejeniyar karshe na ficewar kasar daga Turai.

Frimiyar ta ce kuskure ne tun a yanzu a soma wallafa wani batu, ba tare da kammala cimma yarjejeniyar ba, domin yin haka zai yi tasiri ko haifar da cikas a kokarin da suke wajen kai wa ga matsaya guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.