rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Eritrea Faransa Afghanistan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Arrangama tsakanin bakin haure da jami’an tsaro a Calais

media
Bakin haure a yankin Calais na kasar Faransa PHILIPPE HUGUEN / AFP

A Faransa akalla bakin-haure biyar suka jikkata a birnin Calais na kasar, sakamakon arrangamar da aka yi tsakanin bakin hauren kasashen Afghanistan da kuma Eritria.


Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa yanzu haka, an garzaya da wasu bakin haure 4 ‘yan kasar Eritria asibiti, domin cire musu harsasan da aka harbe su da su.

Fadan wanda bakin hauren suka shafe kimanin sa’o’i 2 suna gwabzawa, ya fara ne a lokacin da bakin hauren ke bin layin karbar abinci.

Kimanin bakin-haure ‘yan kasar Eritria 100 da kuma na Afghanistan 30 rikicin ya rutsa da su.