rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Emmanuel Macron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron zai fara ziyara a tsibirin Corsica da ke neman ballewa

media
A karshen makon da ya gabata ne dubban mutane suka gudanar da zanga zanga a tsibirin na Corsica tare da bukatar tabbatar da dimokiradiya. REUTERS/Zoubeir Souissi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a gobe talata zai fara ziyarar aiki zuwa Yankin Corsica, daya daga cikin tsibirin da ke bukatar karin yanci daga Faransa. Ziyarar ta Macron na zuwa ne watanni biyu bayan da jam’iyyar sa ta sha kayen zaben da akayi a Yankin mai dauke da mutane 330,000.


A karshen makon da ya gabata ne dubban mutane suka gudanar da zanga zanga a tsibirin na Corsica tare da bukatar tabbatar da dimokiradiya.

A wata tattaunawa da ya yi da kafar yada labarai ta RTL a yammacin jiya Litinin, jagoran gwamnatin yankin Gilles Simeoni ya ce suna fatan ziyarar ta Macron ta kawo karshen rikicin yankin da ke neman dawowa ta yadda za ta kafa tarihi ga al’ummar yankin.

Masu fafutukar ganin yankin ya balle tare da samun ‘yancin cin gashin kansa daga Faransa karkashin kungiyar FLNC sun shafe kusan shekaru 40 suna rura wutar rikici matakin da ke barazana ga zaman lafiyar yankin a cewar Mr Simeon.

shekarar 2014 ne aka samu tsagaita wuta bayan wani zaman sulhu tsakanin kungiyar masu fafutukar ballewar da kuma gwamnatin faransa matakin da ya takaita rikice-rikice dama adawar kungiyar ga gwamnatin Faransa.